Read more
Bayan na gama Shiryawa zan fita office sai Amaryata ta fito da shagwaɓa ta rike hannun jakar dake rataye a kafaɗa ta tace "Darling yau a gida zaka zauna kayi min kitso ko" sai na juyo na dubeta tareda dafa kafaɗarta nace " amaryata kiyi hakuri sai na dawo" cikin lallausan murya tace "to My Dear" na tafi har naje bakin kofa sai naji tace " HONEY". Juyowar da zanyi sai tayi min wani kallo mai karya zuciya. Bansan lokacin dana saki jakar dake hannuna ba, nan take nayo kwana, na zauna abakin doguwar kujera nace "zo inyi miki kitson" na ture dan kwalin dake kanta na kama lallausan gashinta ina ja tareda shafawa. Ban ankara ba... Saidai naji saukar Mari,Raassss! na mike a firgice ashe wai mafarki nakeyi, Gemun yayana (Uztaz) da muke maleji a katifa ɗaya na kama inata ja. SADIQ wane irin iskanci ne wannan zaka dinga jamin Gemu ina barci? Yayi ta fada a fusace. Kwana nayi cikin takaici ni ban gama mafarkin ba kuma nasha mari Gwauranta batayi ba kuje kuyi Aure.
Wata Mata tashiga taxi zata unguwa sai ta zauna gidan gaba ana cikin tafiya sai direban ya juy0 ya kalleta da ita da danta sai yayi dariya yace "gaskiya hajiya ban taba ganin mummuna irin Danki ba" sai ta dubeshi tayi tsaki "mtseww" sannan tace ya tsaya ta k0ma baya, tak0ma baya tanata zage zage sai wani ts0h0 dake bayan m0tar yake tambayarta me yafaru sai ta fada masa abinda direban m0tar yace mata sai ts0h0n yace "kin mareshi" sai tace "A'a" sai yace "kaw0 birin dake hannunki in rike maki kije ki mareshi" acikin su wa yafi mata rashin mutunci??
Watarana awani kauye wata bazawara tana da bazawarinta wanda suke shashanci, rannan sai wani daga wani kauyen yazo yace yanasan wannan bazawara. To bayan anyi aure sai yadauke ta yatafi da'ita garinsu. To sai rannan suka hada baki da wancan abokin shashancin nata yace zai yi shigar mata yakawo mata ziyara. ......da yazo sai tace wa mijinta ai kanwar mahaifiyar ta ce tazo sai yayi murna yazo ya gaida ita yaganta kuwa tasha kunshi, sai matar tasa tadau tulu ta tafi rafi debo ruwa.... ...... fitarta kedawuya sai mijinta yazo wucewa... Kwatsam..... sai ya ga wannan bakuwa tayi wawan zama sai kau ya ga ashe namijine!.... haba ai sai gogan naka yadau takobi yabi matar nan tasa rafi a guje.... .....ai ko da matar ta hango shi da takobi a hannu sai kawai ta rafka ihu tana sallallami.....-. Sai gogan naka ya dakata yace me kike wa kuka? Sai tace yanzunna aka aiko min wai duk mazan garin mu sun zama mata, matan kuma sun zama maza. .ai ko da gogan naka ya ji haka sai jikinsa yayi sanyi. Sai yace to wacce kika bari a gida ma ta zama.... Sai kije kigani....
Wata mace ce taje Restaurant don cin abinci . Tana zuwa ta samu all tables din occupied, so bata samu wurin zama ba. Akan ko wane tebur, akwai namiji da matar shi suna cin abinci suna fira cikin nishadi. Da yake ta san halin maza, sai tayi dubara. Ta fito da waya tayi kiran karya, tayi magana da karfi; " Hello Qawata, kiyo sauri ga mijinki a Restaurant ki gani yazo cin abinci da wata". Before you know it, maza takwas sun sulale ba wanda ya sani.
Wata mata ce tana cikin wanka sai taji sallamar abokin mijinta wanda yike makahone sai ta fito Babu kaya a jikinta ta shiga falo ta zauna, ganin cewa makahone sai takirashi ya xauna sai ta dauko kayan kwalliya ba tare da ta lura dashi ba ta fara kwalliya, sai data gama tsaf tasa kayanta daga nan sai ta juyo gareshi don su gaisa, tace masa yazo gaishesu ne? sai yace mata eh dama yazo ne ya gaya mata an masa aikin ido ya samu lafiyar idanunshi yanzu yana gani tangaran.
A Da idan za a yi wa yarinya aure, nasihar iyaye itace "yi nayi bari na bari". Amma yanzu sai dai ace ban da taba masa waya...
Wani bawan allane da matar sa suna kwance, sai matar ta nemeshi, shikuma sanyi yakeji, kuma yana tsoron wankan safe sabida sanyi, tayi tayi akan su raya sunna ya ki, sai ta hakura ta kwanta, can sai ga wani bunsuru yana barbara akofar daki, sai matar tace kaji MAZA. Shiko mijin yace, hm shima dan ba wanka xaiyi bane.
***WASU 'YANSANDA MASU TSORON MUTUWA***
A wata unguwa ce aka wayi gari aka ga wani akwati a wani lungu wadda ake kokwanton bom ne a ciki inji Sa'ad Khalifa Yakubu (Sky) don haka sai aka garzaya aka kira 'yan-sanda da sauri.
Da 'yan-sanda suka zo sai sukayi cirko-cirko aka rasa mai shiga cikin lungun don tsananin tsoro sai D. P. O. Ya tura qaraminsu wai yaje yaga ko zai iya tsayar da bom din kar ya tashi su (dpo) suna daga nesa suna hange.
Qaramin dan-sanda yana kuka yana cewa wallahi yalla6ai ina da iyali da yara qanana a gida da yawa amma zaka tura ni in mutu. Sai D. P. O. Yace yaje ai ba komai don ya sadaukarwa da qasa ransa don za a karrama iyalin nashi idan ya mutu.
Sai Qaramin dan-sandan ya sayar da ransa ya shiga cikin lungun... Yana shiga jikinsa na rawa don tsoro ya bude akwatin sai yaga kudi jibge a danqare a ciki maqil da akwatin. (Ashe wasu 6arayi ne suka sato suka boye a lungun) sai dansandan ya fito a guje yace bom ne ya kusa tashi sai kowa ya hau gudu harda da dpo ogansu.
Da sukayi nisa sai Qaramin dansandan yace wa dpo zai iya qarawa bom din adadin lokaci tashinshi idan za a sami mai iya kawar dashi amma ba zai iya kashewa bane. Sai dpo ogah yace kasan dai ni ogah ne ina da amfani sosai a qasarnan bai kamata inyi ganganci ba, don haka kai kaje ka daukeshi a bayan mashin dinka kaje chan bayan gari ka jefashi a cikin dam don kar ya kashe kowa sai kifaye.
Sai qaramin dan-sanda yace toh shi zai sayar da ransa ga qasarsa nanjeria amma idan ya ku6uta toh yakamata a qara masa muqami zuwa sufeton 'yansanda, sai yace a samo masa buhu sannan yaje ya dauki akwati ya tafi bayan gari ya juye kudin a cikin buhu sannan ya cika akwati da duwatsu ya jefa a ruwa ya dawo gida ya adana kudinsa shi da iyalinsa ya kudance yabar aikin dansanda ya shiga siyasa har aka bashi muqamin minista har ana masa bodyguard harda ogansa dpo cikin masu kula da rayuwarsa masu tsayawa a bayansa.
*KULA DA LAFIYARKA
(yadda zaka wanke kodarka da kanka)
Ka samo ganyen gauta sai ka wanke dakyau kasa a tukunya mai tsafta kasa ruwa mai kyau ka tafasa kamar na tsawon minti goma sai ka sauke ka bari ya huce sai ka tsiyaye ruwan kasha cikin kofi. Lokaci kadan za kaga yadda zai wanke kodarka ka fitsarar da daskararren gishiri da wasu cututtuka su fita daga jikinka kaji garau.
***BARAWO YAYI SATA AMMA YANA MAGIYA***
Wani lebura ne yayi leburanci ya sami naira dubu goma sai ya kai dakinsa ya adanasu yana murna cewa idan gobe tayi zai je garinsu ya taimaki iyayensa da kudin inji sa'ad khalifa yakubu sky sai wani 6arawo ya la6a6a yaje dakin leburan yana barci ya lalube kudin ya sacesu ya gudu.
Toh ashe lokacin da 6arawon yake qoqarin laluben kudin sai wayarsa mai tsadar gaske ta kimanin kudi naira dubu hamsin ta sullu6o daga aljihun barawon ta fadi akan katifar leburan dake barci.
sai bayan da gari ya waye ne 6arawo ya ankara da lallai ya yar da wayarsa a wajen sata a dakin lebura. shi kuma lebura ya soma hada kayan tafiya garinsu sai yaga an sace masa kudinsa dubu goma an bar masa babbar wayar dubu hamsin sai yayi murna kwarai da wannan babban musayan domin kudinsa sun qara auki sosai dalilin satar da akayi masa.
sai barawo ya kira waya yana mai cewa "zan dawo da kudinka dubu goman dana sata don ka bani wayata ta dubu hamsin"
sai lebura yace "ai ka riga ka sayar da wayarka dubu goma, sai anjima"
shikenan lebura ya cire layin wayar barawo ya yar yasa nasa sannan ya ganganda ya sami kudin mota ya tafi garinsu yaje chan ya sayar da wayar dubu arba'in yayi ta facakansa da kudinsa.
-by sa'ad sky.
KULA DA LAFIYARKA
IDAN ZAKA KWANTA BARCI KAR KA RUFE KAI DA BARGO KO MAYAFI SAI DAI KA RUFE GANGAR JIKINKA AMMA KA FIDDO KANKA WAJE DON YIN HAKA ZAI KAREKA DAGA CUTAR DIMAUCEWAR HANKALI WAJEN RASHIN SHAQAR KYAKYKYAWAR ISKA MAI KYAU YAYIN NUMFASHI CIKIN BARCI.
***WATA BUDURWA TASA AN KAMA SAURAYI DON YANA SONTA***
wata budurwa ce tana cikin tafiya akan hanya sai wani saurayi ya tsayar da ita yace mata yana son ya sace zuciyarta sai budurwar ta kwarma masa ihu tace jama'a ku taimakeni ga mai satar mutane. Kafin kace kwabo har an kira kwalawa watau police inji Sa'ad Khalifa Yakubu Sky sun zo sun chafkeshi an kai ofis ana tuhumarsa.
Da aka mayar da ba'asi sai aka tambayeta waye saurayin zai sace? Sai budurwar tace wani saurayinta ne za a sace. Sai akace da yaron da aka kamo kaji abin da tace me zaka ce? Sai yace shi zuciyarta yace zai sace fa, watau ma'anarsa sonta yakeyi. Sai aka ce da budurwar toh ke kinji manufarsa, sai tace eh ai ta gane manufar tasa but amma ai zuciyar tata da yake shirin sacewa ai tana dauke da saurayin nata da take so ne a cikinta shi yisa itama tace masa mai satar mutane tunda zai sace mata zuciyar da masoyinta ke ciki. Daga nan sai kowa ya gane ashe duk abin haukan so ne don haka sai aka koresu suka tafi kowanne yayi nasa wuri.
BABARBARE DA AKUYA.
Wani Babarbare ne ya sayi akuya a
kasuwa, ya kama hanyar gida sai
hanyar ta rabu biyu, da ta gidansa da wata hanyar daban. Yana cikin tafiya sai akuya ta kwace, ta bi hanyar gidansa. Ko da ya ga haka sai ya ce: “Yauwa, ashe dama kin san gidana? To idan kin je ki ce a ba ki dusa ki ci, kafin gama cin kasuwa.”
Wata rana wani Bahadeje ya sayi sabuwar waya (Android), sai ya nuna wa abokinsa. Abokin nasa ya karba ya gani, sai ya fara shiga yanar gizo. Bahadeje ya ce: “Me kake yi ne?” Ya ce masa ai ya shiga Google ne. Ya tambaya: “Mene ne kuma Google?” Abokin ya ce masa ai shi Google wani wuri ne da duk abin da kake nema idan ka rubuta tambaya za su rubuto maka amsa har su nuna maka Bidiyo. Ya gwada masa kuma ya gani. Bayan kwana biyu sai ga Bahadeje ya dawo wurin abokinsa, ya mika masa wayar, ya ce: “Yau Google zai yi mini amfani. kanwata ce mijinta ya yi mata duka har ya fasa mata jiki. Don haka ka shiga Google ka tambaye su, Me ta yi wa mijinta ya yi mata duka? Haka kuma idan da hali har Bidiyo nake son su nuna mini, don na samu hujja, domin in san irin matakin da zan dauka.”
SHAWARAKI!
Wani gardi ne Basakkwace ya je ya yi dako ya samu ’yan kudinsa, ya je ya sayi fura curi goma ya ajiye. Da ya dawo inda ya aje furar sai ya ga
kowace daya an raba ta biyu, sai ya
kama fada yana cewa: “Ni ba satar
ce tai mani ciwo ba, shawaraki da
aka maishe ni.”
Wani saurayi ne ya fito daga gida akan mashin dinsa roba roba yana dan zagaya gari sai ya wata kyakyawar yarinya sai ya kara sa wajenta ya mata sallama ta amsa sannan yace dama sonta yace dan haka ta bashi addrees dinta sai tace ita bata bada addrees sai dai ta bashi numbar wayar ta sai ya amince da hakan, ya dauko biro ya bata yace rubuta min kawai sai ta bude jakarta ta dauko sabuwar naira dubu daya ta rubuta numbar akan kudin ta mika mishi shi kuma yana karba sai ya yage iya inda numbar wayar take ya mayar mata da guntun dubu dayan yayi tafiyar shi Shin acikin ku wayafi jiji dakai da karyar kudi da takama?? SAURAYIN KO BUDURWAR?
JAHILCI!
Wani mutum ne yana zaune da
matarsa mai suna Hamida a gida,
kullum idan ta yi masa laifi sai ya
rika cewa zai sake ta, sai wata rana
da ya gaya mata cewa zai sake ta sai ta ce masa: “Maigida kana saki na shi ke nan sai in je in auri limamin garin nan.” Da jin haka sai maigidan ya zaro ido ya ce: “To da ma ashe liman son ki yake, shi ya sa idan yana Sallah yake cewa ‘sami Allahu liman Hamida?”
DAN DUNIYA.
Wani dan duniya ne ya je wajen
wa’azi, sai ya ji malamin yana cewa: “A karshen duniya mata za su rika yawo tsirara kuma za su rika binVmaza.” Jin haka sai ya buga kafa ya ce: “Wai, Allah Ya kai mu
BAMAGUJE DA BARAYI.
Wata matar Bamaguje ce ta tirka shanu guda biyu sai ta sayar da su, sai 6arayi suka shiga gidansu don yin fashi. Suka samu Bamaguje da duka, da ya ji duka sai ya ce: “Kudin suna gun mai su a ciki.” Sai suka shiga, suka fara dukan matarsa, ta fara ihu tana cewa: “Maigida, maigida!” Shi kuma yana gefe yana cewa: “Ki ba su, kar su kashe ki!”
WASA KO MUGUNTA?
Wani Babarbare ne ya hau babbar mota zai je cin kasuwar qauye. Yana
da sabbin kudi a gaban aljihunsa, ana tafiya kudin suna fita daya-bayan-daya kuma bai sani ba. Ashe wani
Bafulatani yana gani, idan iska ta dauki daya sai ya ce: “Ya yi kyau!”
Babarbare ya ce: “Kai Danfulani, ka dame mu!” Bayan da mota ta tsaya,
ya ce: “Danfulani, sha ruwa ka binne rijiya.” Shi kuwa sai ya yi dariya, ya
ce: “Danborno, tun dazu na ga wasu takardu suna fita daga jikinka.
Babarbare ya duba aljihunsa ya ga babu kudi, sai ya ce: “Danfulani ka cuce ni, tsakanina da kai Allah Ya isa!”
BAHAUSHE MAI WAYO!
Wani Bafullace ne ya ji ’yan uwansa suna ta kuranta cewa Bahaushe yana da wayo, hikima da dabarun rayuwa.
Ran nan sai shiga gari, ya hadu da wani mutum ya ce masa: “Na ji cewa
Bahaushe mayen sani ne, to idan ka cika mayen sani, mene ne a aljihuna?
Idan ka gane zan saya mana abinci da shi. Mutumin ya ce masa kudi ne.
Bafulatani ya je ya sayo abinci, ya zo da kwanon a rufe ya ce masa: “Mene
ne a nan ciki? Idan ka gane zan bude mu ci tare. Shi kuwa sai ya amsa masa da cewa abinci ne. Bafulatani ya ce: “Lallai Bahaushe mayen sani ne, to mu ci.”
ALLAH MAIMAITA!
Wani mahaukaci ne an yi rasuwa wani gida, sai ya zo ya zauna cikin masu karbar gaisuwa. Da aka kawo abinci sai aka zuba masa ya ci ya koshi. Da ya tashi tafiya, budar
bakinsa ke da wuya sai ya ce: “Allah Ya maimaita.”
A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro acikin buhu. Sai suka tsaya suna shawarar inda zasu tafi su raba batare da kowa ya gansu ba. Sai daya ya bada shawarar atafi makabarta,bayansun isa makabarta dauke da mangoro nan, adaidai kofar shiga makabarta sai mangoro biyu suka fado daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada agansu sai suka barsu nan suka wuce cikin makabartar da sauran mangoron. Suna shiga sai suka zube mangoron a kasa suka fara rabawa,babban ne yake rabo. Sai ya dauki daya ya aza agabansa yace"Ni daya"sai ya kuma dauka ya aza agaban karamin yace" Kai daya"a haka suka cigaba da rabonsu.
Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye shayensa,yana zuwa dai dai kofar makabartar sai yaji wata"yar karamar murya kamar ta yara ana cewa"kai daya"ni daya"kuma ancigaba da maimaitawa. Sai kuwa ya garzaya da sauri sai gidan limamin kauyen. Yana zuwa ya sameshi akofar gida yana shirin yin alwalar magariba, yace Allah gafarta malan"yau wani bakon al'amari ke faruwa a makabartar can. Naji ana rabon matattu sai lima yace muje nagani Suna zuwa sai suka labe abakin kofar shiga makabartar,sai sukaji ana cewa"kai daya"ni daya...." can sai sukaji ance"toh kai ga yawan naka nima ga yawan nawa"can kuma sai suka kuma ji ance"Toh wadancan biyun na bakin kofar shigowa fa ? Sai sukaji daya yace toh muje adaukosu mana. Haba!! Ai liman da mashayin nan najin haka sai suka ari takalmin kare,suna fadin aimu bamu mutu ba.
KALLON KWALLO.
Wata rana wani Bafillatani yana kallon kwallo, ya ga ana wasa a fili, ana fasin-fasin. A karshe ya ga duk gudun da suke yi sai ya ga gola yana rikewa kuma ya sake jefawa, sun bi da gudu. Sai ya tambayi na kusa da shi cewa: “Malam, wannan wadanne irin sakarkaru ne, suna ta gudu sun
kasa kama kwallon amma wancen yana tsaye shi kadai ya kama kuma ya sake jefawa, yana hada su fada.
Shin ba su da wayo ne?”
INYAMIRI DA KUDI!
Wani Inyamuri ne ya yi hadari da sabuwar motarsa mai tsada, ya yi
kokari ya tashi ya kira dan sanda ta waya. Da ya iso wurin sai ya ce masa: “Don Allah ka duba ka gani, wannan mai motar ne kawai ya zo ya buga wa sabuwar motata mai tsada, ga shi duk ta lalace.” dan sanda ya girgiza kansa, ya ce wa Inyamuri: “Kai wane irin mutum ne, ta mota kake alhali ba ka lura ba cewa an datse maka hannu, ga shi nan yana ta zubar jini?” Inyamurin nan ya duba ya ga babu hannunsa daya, sai ya saka kuka, ya ce: “Chineke, ina agogona da zobbana na zinare!?”
MARIGAYI
Wani saurayi ne ya amso albashinsa Naira dubu goma da dari biyar,
maimakon ya je ya biya bashin da aka biyo shi, sai ya ki. Ya je ya dauki
budurwarsa zuwa kantin sayar da kayan shafe-shafe, aka zuba mata
duk abin da take so cikin leda ta yi tafiyarta. Da ya zo biyan kudi, sai aka ce am ba ta kayan shafe -shafe na Naira dubu goma da dari biyu. Bayan
ya biya sai aka tambaye shi sunan da za a rubuta a rasidin, sai ya ce a
rubuta ‘MARIGAYI
FUREN KARYA!
Wani ne aka gayyace shi daurin auren abokinsa kuma bai je ba. Washegari sai suka hadu da angon suka gaisa, sai ya ce: “Kai, amma daurin auren nan naka na jiya ya yi mutane. A lokacin nan ina ta miko maka hannu don mu gaisa amma saboda yawan mutane ba ka gani ba.” Shi kuwa angon sai ya yi murmushi ya ce masa: “Allah Sarki, ai ba a daura auren ba ma, an daga sai wani makon mai zuwa, shi ya sa ma na zo domin in sanar da kai.”
AN KI CIN BIRI…
Wata mata ce tana a gaban motar fasinja, sai direban ya ce mata:
“Gaskiya danki yana da muni sosai.” Ina kuma sai ta yi fushi, ta koma bayan motar tana zage-zage sai wani tsoho ya ce mata: “Me kike wa zage-zage? Sai ta amsa da cewa: “Wai direba ne ya ce wa dana yana da muni.” Sai tsohon ya ce mata: “Kin
mare shi kuwa? Ta ce: “A’a.” Sai ya ce mata: “Kawo birin da ke hannunki in rike maki, ki je ki mare shi.”
ARAHAR KOSAI!
Wani Bafulatani ne ya samu mahaifinsa ya ce masa: “Baffa, ina da tambaya! Wai da Wudil da Ladin Makole wacce kasuwa ta fi arahar kosai ne?” Bayan dogon nazari da tunani sai ya amsa da cewa: “To, in dai arahar kosai ne, wannan hai
Wudil, amma in dai ka saya a borka ka dongoli yagi ne, wannan aradu ai
hai Ladin Makole.
MAHAUKACI A KWANA!
Wani mahaukaci ne ya samu wata kwana da mutane suke shiga wurin
fitsari ya tsaya, duk wanda ya rike sai duka. Rannan sai wani soja ya shiga, mahaukacin ya taso sai sojan ya shiga dukansa ba-ji-ba-gani. Da
mahaukacin ya samu ya gudu sai ya tsaya gefen hanya, duk wanda ya zo
shiga sai ya ce masa: “Ka yi hankali fa, akwai mahaukaci a kwana!”
ADDU'A A MAKKAH!
Wani Bafulatani ne ya je aikin Hajji, yana ta faman addu’a, sai ya ji wani
Babarbare a kusa da shi yana cewa: “Ya Allah, duk abin da ka ba wa
Bafulatanin nan, to ka ba ni biyunsa.” sai nan da nan Bafulatanin nan ya
ce: “Ya Allah, Ka manne mini ido daya.”
A GIDAN MATA!
Wani Bafulatani ne ya je gidan mata, sai ya hadu da wani kawunsa. Sai ya
ce wa kawun nasa: “Kawu ni ma na jo!” Kawun nasa ya ce masa: Me ka jo yi?” Sai ya amsa masa da cewa: “Na jo in yi jina!”
AGAJIN LISSAFI!
Wani magidanci ne ya dawo gida sai ya tarar yara suna lissafi, aikin gida da aka ba su a makaranta, lissafi suna cewa: “4+1=5, 4+2=6, 4+3 =7, 4+4, sai suka yi shiru, wato sun manta; sai baban nasu ya ce wa
babba a cikinsu: “Yanzu 4+4 ba ka sani ba? Wawa, jaki!” Sai mahaifiyar yaron ta ce: “Alhaji a gaya masu
mana, ka san yara.” Sai ya ce: “To, a saurara…” Ya dan karkata hula ya ce:
“4+4 amsa biyu ce, in dai ba 40 ba to 44.”
SAKAMAKON ROWA.
Wani magidanci ne yana cin nama a boye, da ganin matarsa ta fito daga daki sai ya tura naman karkashin benci, ya kama wankin karya saboda kada matarsa ta ga abin da yake ci.
Ashe akwai wani kare a bayansa, shi kuma ya samu nama sai da ya cinye duka. Ashe matarsa ta gani, sai da ta
tabbatar karen ya cinye sai ta ce masa: “A gama wanki lafiya maigida.” Ya ce: “To, Allah Ya sa.” Yana jawo takarda sai ya ga ba
komai, sai ya fara salati.
Wani Basakwace ne ya je ya yi bahaya a jeji, yana sanye da jallabiya. Bayan ya gama sai ya ga babu kashi a kasa. Da ya zo cikin jama’a sai ya ce: “Allah Ya yi mini baiwa!” Aka tambaye shi cewa wace irin baiwa ce, sai ya ce da su: “Wallahi na yi tutu ga fili amma ban
gane shi ba.” Ashe kashi yana nan a makale cikin jallabiyar Basakwace, sai
daya daga cikin mutanen ya kalli rigarsa ya ce: “Kai ar takwalli, ga tutu nan na biyarka a riga, har za ka raina mana wayo?
DANGWARI MAI KARYA.
Wani dangwari ne da ma al’adarsu ce idan an haifi yaro sai a rika koya masa karya. To akwai wani rafi kusa da inda ake zuwa koya wa yaro karyar. Sun kama hanya zuwa ke nan, sun zo tsallaka rafin sai baban ya buga ihu ya ce: “Kai, kai yaro, na taka kifi.” Sai yaron ya kada baki ya ce: “Lallai shi ya sa na ji maikon kifin a bakina.” Sai baban ya ce: “Ah, ah, lallai yaro ka yi nisa, bari mu koma gida.”
40 GA RAMALANA.
Al’adar Shehu Jaha a watan azumi ita ce, duk ranar da ya kai azumi sai ya jefa tsakuwa guda cikin wata buta da ya tanada, don gudun kada lissafi ya bace masa. Ran nan sai wata karamar ’yarsa ta ga ya jefa tsakuwar kamar yadda ya saba, da ya fita sai ta ciko hannunta da tsakuwoyi ta watsa cikin butar. Ita a nufinta ta taimake shi ne wajen cika butar da tsakuwa. Ran nan suna hira da makwabtansa sai suka ce da shi: “Yau saura azuminmu nawa ne?” Sai ya ce: “Ban san abin da ya rage ba amma ina sane da kwankin da suka wuce na watan.” Daga nan sai ya tashi ya shiga gida. Da ya kirga tsakuwoyin da yake tarawa sai ya tarar da fiye da 120. A ransa ya ce: “Idan na fada musu wannan adadi dariya za su yi mini amma bari na rage zuwa Arba’in.” Sai ya fita ya ce musu: “Jama’a, yau azuminmu arba’in!” Makwabtan suka tuntsure da dariya, shi ma sai ya shiga taya su, ya kara da cewa: “Ai tsawo ne da wannan wata! To ashe da na fada muku ainihin kwanakin da suka shude a watan, da ban san irin dariyar da za ku yi ba.”
KINA DA RAGO!
Wani kurma ne aka yi masa aure ba ya da cikakkiyar sana’a. Sai matarsa ta haihu aka yi suna a daddafe. Bayan ta yi arba’in wata rana suna kwance sai ta dafa shi. Yana waigowa ya hada ido da ita kina da rago!
BABATA TA FI TA.
Wasu abokai ne suna zaune a majalisarsu, sai mahaifiyar daya ta wuce, sai daya daga cikinsu ya ce, kun ga wannan matar muguwar munafuka ce. Yana juyowa sai suka hada ido da danta. Ya manta yana wurin, sai ya ce amma fa duk munfuncinta babata ta fi ta, saboda babata ba karamar munafuka ba ce, ita ta koya wa wannan
KANURI FI JAHANNAMA!
Wani Kanuri ne ya je aikin Hajji, sai ya shiga ban-daki ya kulle, yana ciki gobara ta kama. Duk Larabawa ne a wajen kuma yana so a kawo masa dauki sai ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Kanuri fin nari!” Ya ji shiru, ya yi ihu da karfi ya sake cewa: “Kanuri fi Jahannama!”
DUK IRINKU NE KUKE JAWO MANA ZAGI A GARI!
Wani mahaukaci ne ya fito yawo kasuwa ba wando ba riga! Kawai sai ga wani mahaukaci shi ma ya zo sai wannan mahaukaci ya hango dayan, ba riga ba wando sai ya kamo hannunsa ya kwada mai mari. Ya ce duk irinku ne kuke ja mana zagi a gari. Sai ya kwabe kayan jikinsa ya ba shi ya sa, sh ikuma ya yi tafiyarsa tsirara. Shin a cikinsu waya fi wani hauka?
MATATA CE A GADO NA BAKWAI!
Wasu maza uku aka kai matansu asibiti wajen haihuwa, daya an kwantar da matarsa a gado na biyu daya a gado na uku, dayan kuma agado na bakwai. Suna zaman jira sai Nas ta zo ta ce wane ne matarsa ke gado na biyu? Sai ya ce “ga ni.” Sai ta ce “Ka yi murna matarka ta haifi ’yan biyu!” Can aka ce “Ina wanda matarsa ke gado na uku?” Ya ce “ga ni” Sai aka ce matarka ta haifi ’yan uku. Wanda matarsa ke gado na bakwai sai ya fashe da kuka. Nas ta ce, “kukan me kake yi Malam?” Sai ya ce, “Matata ce a gado na bakwai!” Wato yana tsoron kada a ce masa ta haifi ’yan bakwai.
YARO KA CE RUWA KAWAI KAKE SAIDAWA!
Wani mutumin karkara ne ya shiga gari ya ji ana cewa a sayi Pure Water mai sanyi, sai ya kira mai Pure Water ya ce a ba shi daya, Da ya bula ya fara sha sai ya jefar ya ce da mai Pure Water kai yaro ka ce ruwa kawai kake saidawa!
DA ZA KIJE INDIYA DA SAI SUN BAUTA MIKI!
Wani magidanci ne matarsa ta yi musu girki, suna zaune suna ci, suna hirar ta miji da matarsa cikin soyayya. Sai mai gidan ya ce: “Gimbiya.” Sai matar ta ce “Na’am Sanyin raina.” Ya ce: “Na rantse da za ki je Indiya sai sun bauta miki.” Sai matar ta ce: “Himm, maigida ke nan saboda kyauna ne? Sai ya ce, “A’a, kawai kin yi kama da saniya ce!”
ALHAJI BA KA BIYA NI KUDIN WANKIN BA!
Wani Alhaji ne yana da mai wanki da guga da yake jin dadin aikinsa saboda ya iya aiki da gaskiya da amana. Wata rana aka kai msa wankin kayan Alhaji da na matarsa da ’ya’yansa. Bayan ya wanke ya goge sai ya shiga ban-daki kafin ya fito, sai barawo ya sace kayan duka. Hankalinsa ya tashi, karshe ya yanke shawarar ya je ya sanar da Alhaji.Yana zuwa ya fada masa abin da ya faru. Matar Alhaji ta yi ta masifa tana cewa sai ya biya. Da kyar Alhaji ya lallashe ta ya ce kada ta damu Allah Ya riga Ya kaddara ko a wajensu suke sai an sace. Sai ya ce wa mai wankin shi ke nan je ka. Amma sai ya ga mai wanki bai tafi ba, sai ya ce za ka iya tafiya ba komai mun yafe. Budar bakin mai wanki sai ya ce, “Alhaji ai ba ka biya ni kudin wankin ba.”
AMMA KA SAN BA YABONKA NAKE YI BA!
Wani Sarkin Fawa ne aka kai shi gaban alkali a kotu, sai alkalin ya yanke masa hukuncin daurin wata shida. Alkali sai ya ga bakin Sarkin Fawa yana motsi kamar yana fadin wani abu a boye. Sai alkali ya ce masa: “Ba zagina kake yi ba dai ko?” Sai Sarkin Fawa ya amsa da cewa: “Amma kuma ka san ba yabonka nake yi ba!”AMMA YA IYA BAYAR DA CARRY OVER!
Wani malamin jami’a ne mai hannu daya ya shiga dakin darasi ya gabatar da laccarsa kan darasin Karin magana. Bayan ya gama karantar da su darasin sai ya ce da daliban idan an fahimta, to kowa zai ba da misalin karin magana daya. Bayan wasu sun bayar sai aka zo kan wata daliba wadda ta daga hannu. Ya ce ta fadi nata: Sai ta ce “Hannu daya ba ya daukar jinka!” Sai malamin ya yi shiru ya dube ta ya ce eh! Amma yana iya ba da ‘Carry over’ (maimaita shekarar darasi) don ubanki!
ALLAH YA ISA.
barawo ne ya sato kaya amma sai wani barawon ya sace, sai ya zo yana ta ’yan dube-dube, jama’a sun ga abin da ya faru amma duk da haka sai suka tambaye shi cewa: “Lafiya kake ta ’yan dube-dube?” Sai ya ki fadin abin da ya faru, sai ya kama kuka yana cewa: “Haka kawai, mutane ba su iya zuwa su yi abu da kansu, sai kai ka je ka yi abu, sai kawai su zo su yi maka abu? Allah Ya isa!”
HASASHE.
Wasu Fulani ne su biyu a cikin azumi suka fita kiwo, suka shiga daji, sun yi kiwo sun gaji har rana ta yi sosai. Da dayan ya gaji sai ya koma inuwa ya zauna a gindin bishiya. Can ya ji cikinsa sai kullewa yake saboda tsabar yunwa, sai ya ce: ‘’Kado, aradu idan muka je lahira, idan na tambaya aka ce azumi bai halatta ba, to ustazan duniya za mu daki uwarsu da sanduna.’’
TURAREN BAFULATANI
Wani Bafulatani ne ya tafi wajen daukar hoto, sai a hanya ya sayi turare ya tafi da shi. Lokacin da za a dauke shi hoton sai ya fesa turaren a jikinsa, da niyyar idan an wanke hoton zai ji kanshin turare a jikin hoton. Ranar day a dawo amsar hoto bai ji kanshin ba sai ya ce: “Ba zan yarda ba sai na ji kanshi tukunna.”
MAI KATOBARA!
Mai katobara ya kasance daga cikin bayin sarki da a ke zaman fada da shi. Ba a taba zaman fada da shi aka tashi lafiya ba, sai ya fadi maganar da za ta sa dogarai su ba shi kasha. Wani lokaci kafin sarki ya cece shi har ya yi tabshi. Wata rana sai ya ce: “Da ma ’yan Boko Haram su kashe sarkin nan a nada wani sabo.” Saboda dukan da aka yi masa kan wannan magana, mai katobara sai da ya yi jinyar sati uku bai zo fada ba. Ranar da ya dawo fada, ko gyaran murya bai yi ba har aka tashi. Can sarki ya mike zai shiga gida, sai wani dogari ya ce: “Yau Mai katobara bai yi magana ba.” Shi kuwa sai ya ce: “Ka ga kuwa sai sarki ya sa a doki gyatumarsa ko?”
BUBA DA ILU.
Buba da Ilu Zazzagawa ne abokan juna amma Buba attajiri ne, sai ya biya wa Ilu Makka. Bayan ya dawo aikin Hajji, sai ran nan suka bata har Ilu ya zagi Buba, sai Buba ya ce: “Tun da ka zage ni, na amshe Makkata, kai yanzu ba Alhaji ba ne, kada a kara kiranka Alhaji, kada ka sake amsawa, daga yau na hana.” Sai wani Bakano ya ba Buba hakuri, sai ya ce: “Na hakura, na yafe masa, na maida masa Makkarsa, ku ci gaba da kiransa Alhaji. Dama bacin rai ne.” Sai Ilu ya yi ta godiya.
0 Reviews