Read more
Wani mai suna Iro mai shayi ne ba ya dawowa gida sai misalin karfe daya na dare. Wata rana yana dawowa sai ya ji ana ta gardama a wani lungu. Ya labe don ganin masu gardama a wannan dare sai ya ga mutum uku ne. daya daga cikinsu ya ce na fi ku sauri, sai sauran biyun suka ce a’a. Sai ya ce to a yi rige-rigen zuwa bangon duniya. Can ya ji shiru kamar minti uku sai ya ji an ce, ni ne na daya, dayan ya ce ni ne na biyu, sai dayan ya ce, ni ne ya kamata in yi na farko amma saboda tuntuben da na yi da dutsen Uhudu ne ya sa na yi na karshe. Iro Maishayi na labe kwatsam sai ya ji an ce to a yi rige-rigen taba kan mai shayi! Sai kawai ya saki zawo a wandonsa.
Wadansu ’yan fashi ne suka tare mota cike da fasinja suka sa kowa ya kwanta a kan titi. Babban barayin ya ci ado, yana zaune. Sai ya ce yau ba wata sata mai yawa za mu yi ba saboda yau ce ranar haihuwata. Kuma sunana Dauda don haka ko mace ko namiji duk wanda sunansa ya fara da harafin ‘da’ sai ya zo ya fada min sannan ya ce min “Happy Birthday!” Wani Basakkwace na zuwa ya ce sunana Duna. “Happy Birthday barawo!”
Wani dan fulani ne matar sa ta kaishi kara kotu.Akan yace cikin da take dashi ba nasa bane. Sai alkali yace to kai kaji abin da matar ka ta fada cewa cikin ka ne. "Sai dan fulani yacewa alkali,Allah ya gafarta malam kai zaka yarda ashe shi daya yana sa mace ta dauki ciki..? To ni shi daya nayi mata,kuma na ganta da ciki sai ashe nawa ne? Sai matar tace kai me gida kaji tsoron Allah.Ka tuna wata rana da ka siyo min tsire da daddare,kashe ka siyo min nama mai dadi. To wannan daren fa..? Sai dan fulani yace to naji shi biyu.Sai matar ta kuma cewa, ka manta lokacin da na kawo maka fura ka sha har kake shewa nafi furar dadi..?To wannan ranar fa?..Sai dan fulani yace to naji shi uku. Sai ta kuma cewa ka tuna naje gidan mu zan kwana kashe bazan kwana ba kaje ka taho dani.To wannan daren fa?..Sai dan fulani yace to naji shi hudu. "Da alkali yaji abin nasu bamai karewa bane sai ya kore su.
INKECE YAZAKIYI??????? KUMA WANE MATAKI ZAKI DAUKA????. Mijinkine yayi sabon Aure, ana cikin Daren amarci,saikiji amarya tana ihu tana kuka Azo aceceta,har gari yawaye baki rintsaba duk abinda sukeyi idonki biyu Kina saurarensu saboda tsabar kishi kinkasayin bacci,kawai saida safiya tayi ,sai mijinki yazo ya bubbuga miki daki,dakin bude sai yace maki,yauwa uwar gidana Dan ALLAH kizoki taimakawa amarya,ki dafa ruwan zafi ki gyarata saboda tasha wuya msosai ammafa akwai dadi ,KUMA inkin gama ki hada break fast ki lallabata taci,yanzu zan dawo inkaita asibati saboda Daren yau .hahhhhha,TO INKECE ME ZAKIYI AKAI??????
Wani bakon baduku ne mai gyaran takalma yana yawo a gari sai wata hajiya ta kirashi don ya dinke mata hancin takalminta inji ni MADOS sai baduku ya shigo har cikin tsakar gida ya fara aikinsa ashe yana mugun nufi akan matar don haka sai ya ciro wani abu ya liqa a takalmin, lokacin hajiya ta shiga daki bata gani ba. Amma ashe wani yaronta mai tsananin wayau yana jikin window ya qurawa baduku ido yana kallonsa bai sani ba.
Chan sai baduku yace hajiya tazo an gama, sai tazo da sauri ta kar6i takalmin zata gwada kenan sai yaron nan nata dake Window ya kwala ihu yace "Hajiya Tsaya, tsaya, kar ki sake ki gwada takalmin nan sai shi badukun ya fara gwadawa an gani" Sai aka ce baduku ya gwada takalmin a qafarsa don a ga me zai faru. Sai baduku yace sam shi ba zai gwada takalmin ba.
Sai mutanen gida kaf kowa ya fito ya taru a wurin aka takura dole sai baduku ya gwada takalmin nan.
Da baduku yaga duk an takura akan dole sai ya gwada takalmi sai ya dauki takalmin nan ya gwada a kafarsa.
Habawa! Ai gwadawarsa ke da wuya sai aka ga...
*MADOS: Kuyi hakuri zan karishe muku labarin anjima don zanci sauran tuwo tukuna sai na gama.
*Jama'a: Haba MADOS don Allah ka karishe mana yanzu muji me ya faru mana!
*MADOS: Nace kuyi hakuri sai anjima mana!
*Jama'a: gaskiya labarin nan ya zama na ban haushi ma!
*MADOS: Ai baku san labarin ban haushi bane don naga duk kowa ya zuro ido kun damu kuji karshen labarina hmmm ai karshen yafi ban haushi ne shi yisa kuka ga na dakata saboda karshen labarin shine WAI ASHE YARON YAGA BADUKUN BAI DINKE TAKALMIN DA KYAU BANE SAI YA MANNE HANCIN TAKALMIN DA CHINGAM DIN DA YAKE TAUNAWA A BAKINSA, DON HAKA NE MA YAKI GWADAWA, AMMA DA AKA TAKURA SHI SAI YA GWADA, YANA GWADAWA KUWA SAI YA TSINKE AKA GANE BAI GYARA TAKALMIN DA KYAU BANE.
karshen kenan fa! sorry fa jama'a don naga kowa ya natsu yaji mummunar karshe ashe na ban haushi ne daman sunan labarin kenan.
***YA KASHE MATARSA***
Wata mata ce mijinta yayi mata kishiya sai uwargidan ta shirya kashe amaryar idan dare yayi suna kwance inji Sa'ad khalifa yakubu Sky don haka da dare yayi sai uwargidan ta sami wani kulki ta la6a6a cikin dakin amarya da aka sakaya ashe mijin na ciki yana lazimi sai yaga mutum da kulki ya shigo cikin dakin amaryarsa sai ya zata 6arawo ne saboda shigar maza da uwargida tayi don 6atar da kamanni. Don haka sai mijin yayi wuf ya chafke kulkin hannun uwargida suka kama kokawa har Allah Ya bashi sa'a ya dabaibayeta ya daga sama ya fyada da kasa har kanta ya rabe biyu nan take ko shurawa ba tayi ba ta mutu murus.
Da aka je wajen mahukunta sai shari'a ta wankeshi sumul luqwi a matsayin 'yar ta'adda ya kashe a bisa kariyar kansa da iyalinsa.
TOH HATTARANKU DAI MATA DA ZAFIN KISHI.
***WATA MATA TA KAMA MIJINTA A CIKIN WAYAR 'YAR AIKINSU***
Wata mata ta dawo daga wajen aikinta sai ta tarar Mijinta bai taso daga wajen nashi aikin ba, sannan ga wayarta ba chaji tana so ta kirashi sai ta dauki wayar 'yar aikin gidan data ajiye kan tebur sai ta sanya lambar mijin nata tayi dialing ta kira. Tana kira sai taga an rubuta "My life" habawa ai cikin tashin hankalin ta kira mijin don tayi mai masifa sai taji mijin ya amsa cikin sanyin murya yace I am sorry my honey ganinan tafe muyi shagalinmu da fatan dai Allah Sa jarababbiyar bata taso aiki ba kar ta kama mu. Ko ban karishe ba dai kuma kun san sauran.
***LABARIN WASU MASOYA BIYU***
Wasu masoya ne saurayi da budurwa suka shaqu sosai cikin soyayyar juna da muradin aure inji MADOS sai kwatsam saurayin ya sami takardan yin karatu a ingila don haka sai ya hanzarta aka sa musu ranar aure da budurwarsa kafin ya tafi. Tafiyarsa keda wuya sai mota ta kade budurwarsa akan hanyarta na zuwa kasuwa wanda a sakamakon haka ta samu matsala na rashin iya magana watau ta kurmance dai duk abu ya dagule mata don ta san saurayinta dake Ingila ba zai ta6a auren kurma don haka sai ta shiga damuwa kullum sai dai kuka. Sai saurayi ya kammala karatu ya dawo yazo gidansu yarinyar inda ya tsaya a gabanta tana ta kuka sai ya sami takarda da alkalami ya rubuta mata kamar haka: Masoyiyata ki bar kuka domin naji dukkan abin da ya sameki toh ki sani nima da naje Ingila qaddara ta sameni na rashin lafiya wadda nima na kurmance sanadiyyar cutar da nayi fama da ita a chan, har na cire ran aurenki sai naji kema kin kurmance shine nazo muyi aurenmu don haka yanzu mun zama daya ki bar kuka. Tana karantawa sai tayi zambur ta tashi da murna ta rungume saurayinta tana murna, haka sukayi auren jin dadi da soyayya cikin kaunar juna kodayaushe. Haka kaddara ke afkuwa ga mutum ya kawo sanadin daza a sake shakuwa na har abada. Allah Yasa muyi kyakkyawar karshe ameen.
SANTIN RAKE.
Wasu Kanawa ne su biyu, suna tafiya sai suka iske wani Bazazzagi a fadamarsa ta rake a Zariya, suka gaishe shi. Shi kuwa sai ya dauki sandar rake guda biyu ya ba su, sai suka zauna kusa da fadamar suna sha. Can sai dayan ya ce: “Da muna da kudi da mun sayi raken nan mun je gida mun yi ta sha.” Shi kuma dayan sai ya ce: “Kai amma da za a yi tashin duniya, da mu kam sai mu shiga fadamar raken nan mu yi ta sha.”
TSUNTSUWA MAI TASHI!
Wani yaro ne ya tambayi uwarsa, ya ce mata: “Mama ni wai don Allah ’yar aikin gidan nan tsuntsuwace mai tashi sama?” Sai ta ce masa: “Haba Sadik, mutum ce ba tsuntsuwa ba ce, ya za a yi ta tashi sama, amma me ka gani?” Sai ya ce mata: “Jiya ne da kika tafi unguwa, sai na ji babana yana ce mata ‘ya ke tsuntsuwar zuciyata!’ Jin haka sai mamar tasa ta ce masa: “Gaskiya ne, tana tashi sama, domin wallahi yau za ta tashi ta tafi kauyensu don ubanta.”
dan kana son ka Burge mace yar Kasar China to kayi Mata Turanci, Idan kana so ka Burge mace Yar kasar India kayi mata rawa, Idan kana so ka burge mace Yar America ka kawo mata (Flower), Idan kana So ka Burge mace Yar England ka zama mai cika Alkawari da Gaskiya. Idan Kana so ka Burge Balarabiya to ka Haddace (Alqur'ani).....
Tambaya:- Wai mai zaka yiwa MACE Yar NIGERIA Don ka Burgeta?
Ina Jiran Amsa.
WANI MUTIMINE YANADA MATA MARAINIYA BA UWA BA UBA.. SE AKA WAYI GARI BEDA KO ASI GASHI GIDAN BABU ABINDA ZA'ACI SEYA FITA NEMAN KUDI YAGAMA ZAGAYA GARI BE SAMO KOMAIBA GA YUNWA GA QISHIRWA NA DAMUNSHI YADAWO GIDA, SE MATARSA TAKE TAMBAYARSA ME GIDA DAGA INA KAKE YACE DAGA LAHIRA NAKE, TACE LAAAAA ASHE KUNHADU DA IYAYENA? SEYACE AE BANBIYO TA WAJEN YAN WUTABA,,,
wani Alhaji ne yaje kauyensu ziyara da motarsa, to ahanyar sa ta dawowa sai dare yaye mass,yana cikin tafiya ne sai yahango wani mutun a gefen titi sai ya tsaya sai mutumin yace Alhaji ataimaka a ragemun hanya zuwa cikin gare sai alhajin yace ya shigo suna cikin tafiya sai Alhaji ya hango kofato a kafar wannan bawan Allah sai Alhaji ya kashe motar sai yace wa wannan mutun Dan fita katoramun motar ta mutu. Sai mutumin yafita yana cikin tura motane sai kawai Alhaji yaye Mata key ya gudu yana cikin tsala uban gudune yayi tafiyar kilometer wajen 50 sai wannan mutun ya leko ta window yace Alhaji har yanzu motar bata tashi ba
.....................in Kaine YAZAKAYI
{ANKI A MIKONI !}
an yi wani bawan allah dan siriri kuma gajere. wanda bashi da wani buri face ya auri kakkarfar mace doguwa kuma mai kiba, anan rannan allah ya amsa rokonsa ya auri wata mata irin mai surar da yake so. bayan an shafe watanni sai ya fuskanci matannan ta raina shi domin sai ta dunga yi masa aike ko bashi umarni irin na yara. aiko rannan sai goganka yace yau sai ya nuna mata cewa shi namiji ne. ya shigowa gida ya zauna sai akayi saa matar tace kai tashi ka debo ruwa zanyi girki. kwatsam sai ya hauta da fada harda kaimata duka. kan kace kwabo ta daga shi sama jikake dammmm sannan kuma ta hau ruwan cikinsa ta zauna kuma ta shake wuyansa. ai kuwa goganka yayi yayi yakasa kwacewa inna sai ya kama ihuuu har saida makota suka shigo suka karbe shi can sai matar tace KU MIKOMIN SHI NAN. ai mutumika sai yada nokewa yana cewa ANKI A MIKO NI.
LAMIDO DA MAI BIREDI.
Waning saurayi ne mai suna lamido yaje gurin mai siyar da biredi ya dauki biredi guda ya matse a hannunsa ya ce mai biredi nawa ne kudin wan an?
Dari biyu kacal inji mai biredi sai lamido ya ce yanzu kudin zan Baka ko kuma na yi ma addu,a ka samu albarka?
Bude bakin mai biredi cewa ya yi bani kudina ka tsine min na lalace
Wata mata ce tanason ta gwada mijinta; taga inhar suka rabu yaya zaiyi?. Sai tadauki takarda tayi rubutu kaman haka; "mijina gaskiya bana sonka yanzu jinake na tsaneka bana bukatar kallon fuskanka gara na kalli fuskan goggon biri da na kalli fuskan ka, bana burin jin muryanka gara na saurayi wakar shata da naji muryanka, dan haka nayi tafiyata ka auro wata"....... Sai ta ajiye akan kujeran da yake falon sannan takoma bayan kujeran ta buya... Mijinta yana zuwa yasamu bakowa a falon yana kokarin zai kirata sai yaga takarda akan kujera sai yadauka yakaranta... Nan take yafashe da dariya sannan ya dauko wayansa ya sa akunnensa yafara cewa, ''hello masoyiyata abun da muka dade muna addu'ar shi yau yazo. Yanzu nadawo daga wajen aiki na samu wannan lalatacciyar matan nawa tabar gidana kinga sati mai zuwa kawai sai adaura mana aure... Sai yafashe da dariya ya kara da yawe kijirani yanzu ina zuwa zamu tafi hotel muci abinci.....'' Bayan yagama maganganunsa sai yajuya bayan takardar yayi rubutu sannan ya bude durowa ya canja riga ya fita yana waka wannan baitin.... ''SOYYAYYA SO MAI SONKA... ZO MUJE MUJEJEJE MUJE MUJE...." Haka ya fita yana wakarsa fuskansa cike da annuri. Fitarsa keda wuya matar tafito tana ta kuka tadauki takardan dan ganin mai yarubuta.... Sai taga yarubuta.....; Kidaina boye-boye Kifito dan nariga naganki abayan kujera, kidafamun ruwan tea yunwa nakeji, naje insayo biredi. cikinsu wa akafi razanawa? 1=Matar....?? 2=Mijin..... ??
HARBIN KUNAMA!
Wani Babarbare ne yana noma shi da karamin dansa sai kunama ta harbi yaron, ya fashe da kuka. Sai kawai ya yi ta marin yaron yana cewa: “Don dan wannan kwaron ya cije ka kake kuka?” Baban ya sa hannu ya kama kunamar zai jefar sai ta harbe shi, ya yi ta tsalle da ihu, yana cewa: “Buba ka yi kuka da kyau sosai, wannan kwaron mugu ne!”
MASHAYA UKU!
Wasu mashaya ne su biyu abokan juna, suka zauna gidan giya da maraice suna ta shan giya har dare ya yi sosai kuma kudinsu sun kare. Suka taho da niyyar zuwa gida, suna tafiya suna tambele da tunkudar juna; farin wata daren sha biyu, ko allura ka yar za ka tsinta. Nan gardama ta kaure tsakaninsu, har rana ta fito. daya na cewa farin wata ne ba rana ba ce, dayan kuma na cewa rana ce. A haka suka hadu da dan wiwi ya bugu, suka ce masa: “Don Allah Malam ka raba mana gardama, wai wannan hasken na rana ne ko farin wata ne?” dan wiwi ya kalle su ya ce: “Wallahi ni ma bako ne amma ku je gaba ku tambayi dangari.
BUZU A KANO!
Wani Buzu ne ya zo Kano sai ya ga yara suna sayen Suwit-kamfo, ya ba da Naira 5 aka ba shi. Yana karba sai ta fadi kasa sai ta dauki datti, ya dauka ya je ya kunna famfo zai wanke ta sai ta narke. Sai ya ce: “Yee, Kano har babu ake sayarwa.”
SAUKA LAFIYA.
Wani Babarbare ne ya shiga mota daga Maiduguri zuwa Bauchi. Da mota ta tashi za a tafi sai wani mutum ya ce a sauka lafiya. Sai Babarbare ya firgita, ya fito daga motar ya ce: “Ku ba ni kudina, ni ba Lafiya zan je ba.” (Ya yi zaton motar garin Lafiya za ta, ta Jihar Nasarawa saboda ya ji an ce sauka lafiya)
DOLAYE BIYU.
Bahadeje ne da Banufe sun je yin itace a daji, kowa ya yo nasa itacen sosai ya dora a kai. Da suka dawo gari, har za su shiga gida ke nan sai Bahadeje ya ce ya manto addarsa a daji. Sai ya koma da itacen nasa a kai, ya je neman addar; shi kuma Banufe ya tsaya jiransa da itacen nasa a kai. Shi ne mutane ke ta gardamar wanda ya fi dolonci a tsakaninsu.
KOMA MALANTA.
Wata rana Jafar da mahaifiyarsa suna hira sai ta ce masa: “Jafar, idan ka gama makaranta wane aiki kake so ka yi?” Sai ya ce: “Ina so in zama malamin makaranta.” Sai mahaifiyar ta ce: “Ai malaman makaranta ba su samun kudi da yawa, ka canza wata sana’ar.” Sai ya ce: “To ina so in zama irin masu zama a mota suna cewa: ‘Samaru Samaru, ana ba su kudi” (yana nufin karen mota saboda yana ganin kudi da yawa a hannunsu). Sai mahaifiyar ta ce: “Jafar, Allah Ya raba ka da karen mota koma malantarka.”
watarana wani barawo yanaso yayi satar mashin, sai ya tare wani dan achaba mai sabon mashin, yace yakai shi police station su dauko dan sanda saboda yanaso suje su kamo wanda ya sace masa mashin dinsa. Dan achaban ya dauke shi suka tafi police station, sai yacewa dan achaban bazai yiwu suyi 3 in 1 ba su uku, saidai dan achaban yabasu mashin din suje da dan sandan domin su kamo barawon. Sai dan achaban ya basu mashin suka barshi a police station yana jiransu. Isarsu kasuwar mashin ke da wuya, sai wannan barawon daga nesa ya nunawa dan sandan nan wani mutum yace shine barawon mashin dinsa, saboda haka yacewa dan sandan yaje ya kamo shi, saboda in barawon yagansu tare zai gudu. Tafiyar dan sandan ke da wuya domin yaje ya kamo wanda akace masa barawon mashin ne sai wannan barawon ya buga mashin kawai ya kara gaba. to in kaine dan sandan ya zakayi?
'YAR ZARIYA.
Wata 'Yar Zariya ce ta je Makka har sau uku amma kawarta ba ta kiran ta da Hajiya sai dai ta kira ta da sunanta na asali. Abin ya dame ta sai rannan ta yi wa kawar tata nasiha, ta ce mata: “Kin ga fa Arafata ukku, jifata ukku amma ba ki ce mani Hajiya, sai dai ki kira ni da ’Yar Zariya. To, ki ji tsoron Allah, ki tuba ki daina. Kina halaka kanki ne ba ki sani ba, kada ki mutu ki ci wuta. Ke ba ki kirana da Hajiya, yanzu ranar gobe kiyama ina za ki da wannan zunubin?
Wani Daga Cikin Bayin ALLAH Magabata Ya Ce:-
"Naga Wani Makeri Da Yake 'Dauko Karfe Daga
Wuta Da Hannun Shi, Bayan An Zuga Karfen Ya
Zugu, Amma Kuma Baya 'Konewa.
Sai Na Tambaye Shi Game Da Haka,
Sai Makerin Nan Yace:'Na Kasance Ina
Makwabtaka Da Wata Kyakkyawar Mata, Kuma
Zuciya Ta, Tuni Ta Kamu Da Son Wannan Mata,
Amma Na Rasa Hanyar Da Zan Bi In Samu Sa'ar
Ta, Saboda Tsantseninta Da Kuma Kamun Kanta.
Sai aka yi fari(karancin ruwan sama) a wannan
shekara, kuma abinci yayi wahala. Sai wannan
mata ta zo waje na tace mani: Ka ciyar da ni
wani abu saboda ALLAH!
Sai nace: har sai kin yarda da ni.
Sai tace: ba zan iya sabawa ALLAH ba.
A rana ta biyu ma, sai tace mani:
ka ciyar da ni wani abu saboda ALLAH. Sai na
bata irin amsar farko. Sai taki yarda.
A rana ta uku ma, tace mani: ka ciyar da ni wani
abu saboda ALLAH hakika yunwa ta fara chutar
da ni.
Sai na sake fadi mata abinda na saba fada tun
farko.
Sai ta shiga gida na, na kawo kayan abinci
daban-daban na aje a gabanta. Sai ta fashe da
kuka, tace: ka ciyar da ni domin ALLAH. Sai nace
mata a'a. Sai ta fice abinta tana kuka.
A rana ta hudu, tace mani: ka ciyar da ni wani
abu domin ALLAH. Sai ta sake shiga gida na. Sai
na je na kawo mata kayayyakin abinchi.
Sai ALLAH ya riskar da ni da ludufin shi, sai nace
a cikin raina: Wannan mata ta hana kanta
sabawa ALLAH tare da tsananin halin wahala da
take ciki, amma ni na kasa in hanu tare kuma da
halin walwala da nake ciki, YA ALLAH INA TUBA
ZUWA GARE KA. sai nace mata kwashe dukkan
kayayyakin abincin nan ki tafi kada kiji tsoro na
baki saboda ALLAH.
Sai tace:"YA ALLAH IDAN DA GASKE YAKE, TO KA
HARAMTA SHI DAGA KUNAR WUTA DUNIYA DA
LAHIRA".
-------
Ya ALLAH! Muma Muna Rokonka, Ka Haramta
Wuta Garemu Duniya Da Lahira AMEEEN

0 Reviews