Natsuwar Zuci

Natsuwar Zuci

Size:
Price:

Read more



Tambaya :

Don Allah malam ta yaya zan samu nutsuwa
a cikin zuciya ta?, saboda wani lokacin sai
na ji zuciyata, kamar an kunna min wuta,
wasu lokutan kuma bakin ciki ya hana ni
bacci
Amsa :
To dan'uwa akwai abubuwan da malamai
suka yi bayani cewa : suna kawo nutsuwa a
zuciya, ga su kamar haka :
1. Cikakken tauhidi, ta yadda mutum zai bar
duk wata shirka da bidi'a da abin da yake
kaiwa zuwa gare su .
2. Shiriya da hasken da Allah yake jefawa a
zuciyar bawa, wanda duk lokacin da aka
rasa shi, sai bawa ya kasance cikin kunci.
3. Ilimi mai amfani, saboda duk lokacin da
ilimin mutum ya yalwata, zai samu jindadi a
zuciyarsa.
4. Dawwama akan zikirin Allah, saboda fadin
Allah "Wadanda suka yi imani zuciyoyinsu
suna nutsuwa da zikirin Allah" Suratu
Arra'ad aya ta 28
5. Kyautatawa bayin Allah, saboda duk
mutumin da yake yin kyauta zai kasance
cikin kwanciyar hankali, kamar yadda
marowaci yake kasancewa cikin kunci.
6. Fitar da kyashi da hassada daga zuciya.
7. Barin kallo da zancen da ba shi da fa'ida.
8. Barin baccin da ba shi da amfani.
9. Cin abinci gwargwadon bukata, da rashin
karawa akan haka.
10. Rashin cakuduwa da mutane sai
gwargwadon bukata.
Kishiyoyin wadannan abubuwa su ne suke
jawo bakin ciki da damuwa da kuma kunci.
Don neman karin bayani duba zadul-ma'ad
2\22
Allah ne ma fi sani

0 Reviews

Contact form

Name

Email *

Message *