Read more
Ance wai akwai wani lokaci da Mahaifiyar wani Tsohon Gwamnan jihar, mai suna Col. Oneya, ta rasu. Kamar yadda akeyi a al'ada, sai aka je harda shi Gwamnan domin yi wa marigayi Sarkin Kano Ado gaisuwar uwar Gwamnan. Kafin a tashi, sai shi Gwamnan da kanshi ya nemi Sarki yayi wa uwar ta sa addua. Sarki dai yayi shiru, ya ga dai gashi kuma ba Musulma ba ce balle ayi mata adduar da akan yima mamaci. Bayan ya nisa, sai Sarki ya dubi Dan Masanin Kano, Amb. Yusuf Maitama Sule ya ce, Dan Masani, ai sai a yi Mata addua. Ba tare da wani jinkiri ba, sai Danmasani ya ce a karanta Mata Charmandudu da Danmaliyo kafa bakwai, bakwai, Allah yayi Mata abinda ya da ce da ita. Da kyar Mai Martaba ya gintse dariya. Allah Ya jiqan Ado Bayero, Allah Ya jiqan Yusuf Maitama Sule.
Bayan na gama Shiryawa zan fita office sai Amaryata ta fito da shagwaɓa ta rike hannun jakar dake rataye a kafaɗa ta tace "Darling yau a gida zaka zauna kayi min kitso ko" sai na juyo na dubeta tareda dafa kafaɗarta nace " amaryata kiyi hakuri sai na dawo" cikin lallausan murya tace "to My Dear" na tafi har naje bakin kofa sai naji tace " HONEY". Juyowar da zanyi sai tayi min wani kallo mai karya zuciya. Bansan lokacin dana saki jakar dake hannuna ba, nan take nayo kwana, na zauna abakin doguwar kujera nace "zo inyi miki kitson" na ture dan kwalin dake kanta na kama lallausan gashinta ina ja tareda shafawa. Ban ankara ba... Saidai naji saukar Mari,Raassss! na mike a firgice ashe wai mafarki nakeyi, Gemun yayana (Uztaz) da muke maleji a katifa ɗaya na kama inata ja. SADIQ wane irin iskanci ne wannan zaka dinga jamin Gemu ina barci? Yayi ta fada a fusace. Kwana nayi cikin takaici ni ban gama mafarkin ba kuma nasha mari Gwauranta batayi ba kuje kuyi Aure.
KARYA FURE TAKE. wani abokin ango ne aka gayyace shi daurin auren abokin sa bai jeba washegari sai suka hadu da angon suka gaisa sai yace kai amma daurin auren yayi mutane ina ta miko maka hannu baka ganiba sai yace ai an daga sai wani satin.
Asha dariya, Wani yarone babarsa ta aikeshi, shago da naira ashirin goma goma guda biyu,suga na goma ganyenshayi na goma,da yaran yaje shagon sai yasamu waje yazauna yana kuka, sai aka tambayeshi lafiya yake kuka ko kudinne suka fadi, sai yaron yace a'a mantawa yayi wacce gomace ta suga waccece ta ganyenshayi .
Wata yarinya ce taga hoton babanta lokacin ana samartaka an ci tabarau, ga uban gashi da matsattsiyar riga, wandon nan fantalo; kawai sai mamanta taji ta tana dariya. Sai uwar ta tambayeta "menene ya ke saki dariya haka?"
Yarinya kuwa ta ce "Hoton baba na gani lokacin yana dan iska"!!!
ANGO MAI FITSARIN KWANCE
wani ne yayi aure yana fitsarin kwance, ya kwanta bacci sai yayi fitsari ya rasa yadda zaiyi kawai sai ya tada matar yace mata " idan kece kikayi mafarkin kura da zakida damisasu biyoki ya zakiy?sai matar tace"tabdijam ai sai nayi zawo, sai angon yace ashe ni jarumine fitsari kawai nayi
***WATA YAYA TAYI SAKE QANWARTA TA AURE MATA MIJI TANA KALLO***
Wani Ango ne daga yin aurensu ba dadewa sai amaryarsa ta shiga kafta masa rashin mutunchin da har ya kasa jurewa ya kai qararta wajen mahaifinta inji sa'ad khalifa yakubu sky sai mahaifin nata ya kirata yaja mata kunne yayi mata fada amma duk tayi kunnen shegu ta ci gaba da rashin mutunchinta ga mijinta bata daina ba.
sai ango ya kara samun mahaifin nata, toh anan sai mahaifin yace wa mijin ya korota ta dawo gida, bayan kwana biyu sai yazo. haka akayi bayan kwana biyu sai mijinta yazo gidan su amaryar tasa, sai mahaifinta ya tarasu kamar zai musu fada amma sai ya umurci angon ya saki 'yar tasa watau amaryar har saki uku. sai yaron ya saki amaryar kamar yadda babanta ya umurceshi. daga nan sai babanta ya kalli yarinyar watau amarya yace toh ita kuma ta zauna anan gidan iyayen kar ta sake ta koma tace zata dauko koda tsinke ne a cikin kayan aurenta dake gidan mijin. sai uban ya kira qanwarta yace wa mijin ga qanwarta nan ka nema in baka don tafi yarta hankali.
sai yaro watau mijin ya nemi qanwar matarsa da ya saka ya biya sabon sadaki aka daura masa aure da ita ta shige dakin yayar tata ta gaje dukkan kayan auren nata ta zauna daram sukayi zaman jin dadin aure mai dorewa. aka bar yayar tata da cizon yatsa cikin takaici da dana-sani mara amfani.
***RANAR BIYA TA ZO***
Wani Matashi ne babansa yayi masa fada akan mugayen dabi'unsa, sai matashin ya hau zagin mahaifin nasa har ya kamashi da kokawa ya kayar dashi kasa ya daga hannu zai nusheshi kenan sai kakan matashin yazo a guje ya riqe masa hannu yace rabu dashi hakanan domin nima da ya kayar dani kasa bai nusheni ba.
*ME KA GANE ANAN?
***IYAYE KAR KU YIWA 'YA'YA AUREN DOLE***
wata budurwa ce ta kai wa babanta saurayin da take so don a aura mata shi amma sai babanta yace mata sam ba zai aura mata shi ba saboda bashi da komai talaka ne sosai wai sai dai ta auri abokinsa Alhaji Barau. Bayan wasu watanni Sai budurwar ta shirya wata dabara inda taje gida tayi ta qaqaro amai tana zubar da miyau sannan tace wa iyayenta bata ga al'adanta tun watanni biyu baya ba ma'ana dai wai tana da ciki kuma saurayin da take so yayi mata.
Da iyayenta suka buga suka ga ba wata mafita sai suka kira saurayin aka daidai akace ya dauketa yaje a zubar yazo a daura musu aure don a rufa wa kowa asiri tunda iyayen yarinyar duk talakawa ne gaba da baya.
Sai bayan anyi auren ne sannan yaran watau maauratan suka zo suka sami iyayen don neman gafararsu cewa qarya suka shirya musu amma ba wani ciki da yarinyar tayi just sunyi qaryar haka ne ita da saurayinta don dai iyayen nasu su daura musu aure kawai amma samsam koda wasa basu ta6a kusantar juna kafin aure ba. Sai baban kunya ta kamashi sannan ya yafe musu ya albarkaci auren.
***WANI MOTSATSTSE YA BA WANI 'DAN-KWAYA AMSAR TAMBAYARSA***
Wani malami ne yana wa'axi a sai ga wani dan shaye-shaye ya bugu yana wucewa, da ya juya ya kalli ana wa'axi sai yace; "yauwa! daman inada tambaya" sai ya juya yanufi inda ake wa'axin, yana xuwa sai yace abashi hanya
aka hana shi shiga yatayar musu da masifa da malam yaga abinda kefaruwa sai yace: "abarshi ya shiga" Yana xuwa yafadi gaban malam sai yace; "Allah gafarta malam inadatambaya" Malam yace: "inajinka" sai yace; "malam ba kasan mata suna nika akan dutse ba?" malan yace hakane sai yace; "toh malam idan suna nika wake akan dutse wannan k'aran dayake fita gurus gurus gurus dinnan shin daga jikin dutsen k'aran yake fitane ko daga waken ne yake fita? Daman akwai wani motsatstse dayake xaune a wurin, da motsatstsen yaji wannan tambayan sai yatashi ya wanke mai tambayan na da mari fas! sannan yace; nima bari inyi maka tambaya wannan marin da nayi maka 'karan da ya fitan nan shin daga hannunane ko daga kumatunka ne k'aran ya fito? sai 'Dan-kwayan ya tashi cikin fushi ya tafi bai amsa ba.
***WATA YARINYA MAI KWADAYI DA WANI GAYE MAI WAYAU***
Wani saurayine yaga wata kyakykyawar yarinya a tsaye ita kadai tana wasa da babbar waya a hannunta sai MADOS wanda ke baku wannan labarin yace sai saurayin ya matsa kusa da yarinyar ya dan kashe muryarsa don ta kara zaqi yace mata ya ganta fa yana so, ya za ayi yanzu?
Sai yarinyar tace ai kawai zuwa za muyi waccan "restaurant" din (watau wajen sayar da abinci) don muyi magana yadda zan fahimceka sosai.
Sai kuwa suka dunguma suka je suka shiga suka zauna sai aka taryesu da cewar wane kalar abinci za a kawo musu? Ai kafin saurayin ya tanka tuni yarinyar tace a kawo mata farfesu da juice watau ruwan lemo da saurayin yaga haka sai yace shima a kawo masa irin nata sai duk aka kawo musu har yarinyar na murmushi tana cewa saurayin kaga munyi ankon farfesu ko? Saurayi yace eh sannan ya farmaki farfesun kajin nan cikin sauri baji ba gani ya cinye cikin sauri, ita kuwa yarinyar tana ta faman yanga da feleqensu na mata don taja aji sai taga ya cinye amma yaqi shan juice din ya kura masa ido kawai yana kallonsa sai tace darling toh kasha juice din mana ko baka son irinsa ne a chanzo maka?
Sai saurayin yace yana so mana, amma dai ita ta dauki nasa duk ta hada ta shanye ba zai sha ba.
Sai yarinyar tace don me?
Saurayin yace don shi yana son sha amma fitsari ne ya matse shi kamar zai fasa mararsa ya fito da karfin tsiya.
Sai ya yarinyar tace haba darling in don haka ne toh kaje waje mana kayo fitsarin kazo kasha don ya zama muna sha a tare iron na masoya.
Sai saurayin yace mata toh, sai kuwa ya fita waje ya sulale ya gudu ya barta nan.
Shiru-shiru bai dawo ba, sai masu abinci suka ce ai sai ta biyasu kudin abincinsu mai tsada na naira dubu goman da suka yi oda da saurayinta.
Yarinya ta shiga kuka tana cewa Wallahi ban sanshi ba fa.
Amma masu abinci suka yi banza da ita suka kar6e wayarta mai tsada da wani gara shima ya saya sannan suka koreta waje tana kuka.
***TACI MUTUNCINSA SHI DA KAYANSA***
wata budurwace taje filin jirgin sama (airport) don shiga jirgi zuwa wata kasa amma lokacin tashinsu bai yi ba sai ta sayi wani biskit na alfarma ta sami wuri ta zauna don taci kusa da wani dattijo da shima yake jiran jirgin inji MADOS
sai tasa hannu ta dauki biskit kwara daya ta kai bakinta sai kawai taga shima dattijon nan yayi farat yasa hannu ya dauki daya shima ya kai bakinsa yana mata murmushi, sai ta kara dauka shima ya kara dauka. haka su kayi tayi tana dauka yana dauka sai daya ya ragu sai dattijon nan ya dauki dayan sannan ya gutsurashi gida biyu ya dauki daya rabin ya ajiye mata daya rabin. abin ya bata haushi ta rasa abin da zata ce don haushi sai ta shiga kunduma mashi zagi ta uwa ta uba amma shiko bai ce uffan ba hasali ma sai murmushinsa yake yana mai sukuyad da kansa har ta gaji ta tafi.
bayan ta hau jirgi kuma ya tashi sama da ita sai ta dauko jakarta don ta gyara 'yar kwalliyarta kwatsam sai taga biskit dinta a ciki ko 6areshi bata yi ba, mamaki ya kamata, can sai ta tuna ashe data saya ta saka a cikin jakartane kuma wanda suka ci tare da tsohonnan wadda tayi ta zaginshi akansa ashe na tsohon ne shi ya saya da kudinsa, ya barta ta cinye masa sannan ta zazzageshi akan abinsa.
take sai kunya, tausayi da nadama duk suka zo mata don gashi ta nufi wata kasa da kila ma baza su sake gamuwa da tsohon ba balantana ta bashi hakuri..."ALLAHU AKBAR, LALLAI ALLAH YANA TARE DA MASU HAKURI, SANNAN S.A.W. YACE KAR MUYI FUSHI.
***ALMAJIRI DA ATTAJIRI***
Anyi wani almajiri wanda yaje wani gari neman ilimi sai ya sauka a gidan wani attajiri mai wadata inda aka bashi masauki a zauren gidan MADOS ya kan fita kasuwa yin dako sannan idan ya dawo yaje ya dau karatu sannan ya dawo masaukinsa ya kwana. Yin hakan tasa har Alhajin ya yarda dashi yake masa 'yan aike-aike yana biyansa ladan kudi da abinci sai dai matar Alhaji bata da kirki ta tsaneshi kullum so take a koreshi bata bashi abinci har sharri take kulla masa don a koreshi amma Alhaji ya aminta dashi kwarai suna tare. Wata rana sai karayar arziki ta sami Alhajin har komai nasa ya kare sai gidan, hakan tasa dole aka daga gidan a kasuwa za a sayar. Sai Alhaji ya gayawa almajirin nan yayi hakuri ya fita zai sayar da gidan da suke ciki, sai almajiri ya tambayi kudin gidan aka gaya masa sai aka ga yaje banki ya ciro kudi ya biya kudin gidan sannan yace Alhajin yaci gaba da zama har kafin Allah Ya hore masa ya sake sayen nasa na kansa, shi kuma almajirin yaci gaba da zama a zaurensa yana fita dako da karatunsa yana samo kudi yana ciyar da Alhajin da muguwar matarsa mai hanashi abinci sai ya saka mata sharrinta da Alkhairi saboda kyakkyawar mu'amularsa da Alhajin bisa Ilimin dake gareshi hakan tasa taji kunya tare da gyara munanan halayenta ta gyara dabi'unta.
KOYARWAR LABARIN SHINE YAKAMATA MU DINGA SAKA WA MUTUM DA ALKHAIRI KODA YAYI MANA SHARRI.
***BARAWO YA KAMA KWARTO***
Wani barawo ne ya shiga gidan wani maigida da yayi tafiya ya bar matarsa kadai ashe tana tare da wani katon kwarto suna sheqe aya MADOS sai 6arawo ya fado dakin kwatsam sai kwarto ya dauka maigida ne ya dawo sai ya zaburo tsirara da gudu zai yo waje sai 6arawo ya dauka kamashi za ayi sai ya kai nushi suka kama kokawa sai matar tsoro ya kamata bata san lokacin da ta kwarma ihu mutane suka shigo ba, ta manta tana tsirara ba kaya a jikinta haka mutane suka samesu aka kama kwarto amma banda barawo don bai dauki komai ba sai godiya ake masa da ya kama katon domin an dauka kwarton fyade zai yiwa matar da karfi shine 6arawon ya kawo mata dauki da ya ji ihunta kafin mutane su qariso yazo ya taimaketa.
***ASHE TASO TACI BANZA NE***
Wani saurayine yaga wata kyakykyawar yarinya a tsaye ita kadai tana wasa da babbar waya a hannunta sai MADOS watau wanda ke baku wannan labarin yace sai saurayin ya matsa kusa da yarinyar ya dan kashe muryarsa don ta kara zaqi yace mata ya ganta fa yana so, ya za ayi yanzu?
Sai yarinyar tace ai kawai zuwa za muyi waccan "restaurant" din (watau wajen sayar da abinci) don muyi magana yadda zan fahimceka sosai.
Sai kuwa suka dunguma suka je suka shiga suka zauna sai aka taryesu da cewar wane kalar abinci za a kawo musu? Ai kafin saurayin ya tanka tuni yarinyar tace a kawo mata farfesu da juice watau ruwan lemo da saurayin yaga haka sai yace shima a kawo masa irin nata sai duk aka kawo musu har yarinyar na murmushi tana cewa saurayin kaga munyi ankon farfesu ko? Saurayi yace eh sannan ya farmaki farfesun kajin nan cikin sauri baji ba gani ya cinye cikin sauri, ita kuwa yarinyar tana ta faman yanga da feleqensu na mata don taja aji sai taga ya cinye amma yaqi shan juice din ya kura masa ido kawai yana kallonsa sai tace darling toh kasha juice din mana ko baka son irinsa ne a chanzo maka?
Sai saurayin yace yana so mana, amma dai ita ta dauki nasa duk ta hada ta shanye ba zai sha ba.
Sai yarinyar tace don me?
Saurayin yace don shi yana son sha amma fitsari ne ya matse shi kamar zai fasa mararsa ya fito da karfin tsiya.
Sai ya yarinyar tace haba darling in don haka ne toh kaje waje mana kayo fitsarin kazo kasha don ya zama muna sha a tare iron na masoya.
Sai saurayin yace mata toh, sai kuwa ya fita waje ya sulale ya gudu ya barta nan.
Shiru-shiru bai dawo ba, sai masu abinci suka ce ai sai ta biyasu kudin abincinsu mai tsada na naira dubu goman da suka yi oda da saurayinta.
Yarinya ta shiga kuka tana cewa Wallahi ban sanshi ba fa.
Amma masu abinci suka yi banza da ita suka kar6e wayarta mai tsada da wani gara shima ya saya sannan suka koreta waje tana kuka.
Wata ranar juma’a liman ya makara, sai wani mahaukaci ya zo ya hau kam mimbarin, sai wasu daga cikin masallata su kayi kokarin saukar da shi kasancewar sun gan shi mahaukaci, sai aka yi dace daya daga cikin masu kula da masallacin yana nan, sai ya ce kubar shi yayi hudubar in ya sauko liman yayi tasa.
Ga Yadda hudubar mahaukacin ta kasance kamar haka…
Ya ce dukkan godiya ta tabbata ga wanda ya halicceku iri biyu, sannan ya raba ku gida biyu, ya sanya masu wadatarku don su zamto masu godiya, sannan yasanya talakawan ku don su zamto masu hakuri, sai aka yi rashin dace, masu kudin basa godiyar sannan talakawan basa hakurin…
Allah ya tsine mu ku gaba daya….ku tashi ku yi sallar….
Shin abunda wannan mahukacin ya fada gaskiya ne kuma me, ka fahimta?
wata rana dan fulani ya shiga mota xaije wani gari toh, ana cikin tafiya ashe dan fulani yananan ya kallon mai mota yanatasa giyar motarshi, idan yasa ta 1 sai ya murza ta takoma a ta 2 idan ta 2 ta shiga sai ya sa ta 3 haka dai danfilani yake ta ganin yanda mai mota yake ta fama dasa giyar motar shi, wani daga cikin motar sai ya ce yana jinfitsari atsaya zai yi aka faka mota gefen titi ana tsayawa kowa ya fita cikin mota yana yin abunda yadamai, shi kuma gogan na ka yana ciki bai fito ba kawai sai yafa kai ci idon mutane yakama wannan giyar mota yacigaba da girgizata, yana cikin girgiwa kawai sai Allah ya taimake shi yana cikin hakan kawai sai giyar mota tatunbuko gaba dayanta kawai saiga mai mota yana zuwa, sai dan Fulani yace an shi abunda kaketa fama kashiro tun dazun kaka sa toni gani na shiro maka shi anshi
Wani mahaukacine ya zo wucewa, sai ya ga ana zaman makoki, sai ya zauna akayi addu’a da shi, ba yan angama sai ya tambaya, mace ce ko namiji?, sai aka ce masa namiji,
Sai ya ce babba ne ko karami? sai aka ce masa yaro ne,. Abin ka da gogan na ku sai ya ce, Allah!! shi kara, watakilma dashi ake tsokanata
TSINTUWAR KUDI.
Wani mutun ne talaka ya wayi gari ba kudi ba abinci, sai ya ce wa matarsa ta jira zai je kasuwa ya dawo. Da fitowarsa kofar gida sai ya yi addu’a ya ce: ‘’Ya Allah Ka sa na tsinci Naira dubu biyu. Idan har Ka ba ni Naira dubu biyu, ni kuma zan ba da Naira dubu daya sadaka fisabilillahi.” Yana cikin tafiya har ya kusa zuwa kasuwa sai ga Naira dubu daya a kasa. Ya duka ya dauka cike da murna sai ya ce: “Oh, Allah gwani cikin ikonSa ka ga har Ya dauki nasa kason!”
ALLAH KAWO RUWA.
Wani Inyamuri ne aka wayi gari da ruwan sama har yamma ba a dauke ba, bai samu damar bude shagonsa ba. Da dare, bayan ruwa ya dauke sai ya bude shagon yana kasa kaya, sai ga wani Bahaushe ya zo sayayya. Can sai aka buga walkiya da tsawa, Bahaushe ya ce: “Allah kawo mana ruwa!” Cikin fushi Inyamurin nan ya ce: “Wanda aka yi tun da safe, me ka yi da shi?”
TAKAICIN MATA!
Wani sarki ne a Bida, matarsa ta bata masa rai, ya rasa abin da ke masa dadi, ya fita zuwa fada cikin bacin rai. Yana zuwa sai ya tarar da mutane suna ta hayaniya a waje, ya tambayi lafiya? Aka ce masa: “Wani mutum ne ya kashe matarsa, aka kawo shi wajenka ’yallabai.” Sai sarkin ya ce: “Ku sake shi, ya kashe banza.”
TSARIN IYALI.
Wani mutum ne ya je gidan gona ya sayo kwan kaji, ya kawo wa matarsa cewa ta soya masu. Ta shiga kicin ta fara fasa kwayayen amma kowanne ta fasa sai ta ga babu ruwan kwan a ciki. Da mijinta ya dawo ta gaya masa sai ya yi mamaki, ya dauki kwafsan kwayayen ya koma gidan gona ya shaida wa manajan abin da ya faru. Manaja ya yi mamaki, ya shiga dakin kaji yana cewa: “Aikin wofi, kowane kwai kuma ya zama ba komai ciki!” Sai ya ji kaji sun amsa masa suna cewa: “Maigida, ai mun gano sirrin abin, mu ma Family Planning (tsarin iyali) muka fara.”
DA KA TSAYA DA NA FASA MAKA KAI DA SHANTU!
Wani kwarto ne ya je gidan abokiyar harkarsa, kwarto na leka dakin matar ta taga ya hange ta kan gado, yana matsawa sai ya bugi tiren kwanuka, maigida na ban daki, sai ya rugo da gudu su ka yi arba da kwarto. Kwarto ya ranta a na-kare mai gida ya bi shi da katon abu a hannunsa. Suna cikin gudu sai maigidan ya ce “Da ka tsaya da na faffasa maka kai da wannan shantu!” Koda kwarto ya ji ashe shantu ne a hannun maigidan sai ya tsaya ya ce: “Da ma shantu ne a hannunka, nake ta gudu kamar raina zai fita!” Sai kwarto ya juyo kan maigida, ganin haka maigida ya juya da gudu da kyar ya kai gida da gudu da roron wake.
TSOHUWA DA SAURAYIN JIKARTA!
Wani saurayi ne ya ga wata budurwa ya ji yana sonta da aure, sai ya tambaya aka shaida masa cewa tana hannun kakarta ce. Sai ya je gidan don su gaisa, ya shaida mata cewa: “Inna, Maryam ce na gani nake so da aure.” Sai tsohuwa ta ce: “A’a yaro an ba da ta.” Da zai tafi sai ya ciro damen kudi sababbi ya mika mata ya ce ta sayi goro. Da ta ga kudi cus, sai ta ce: “tsaya yaro, kai dan gidan wane ne?” Ya ce shi dan gidan Malam Haruna ne. Ta ce na wajen Malam Saleh, ya ce, eh. Ta ce: “Allah Sarki! Malam Saleh mutumin kirki ne, lokacin da muke yara idan muka ja fada shi ke tare mana!
MAKABARTAR DA AKA KAI NI CE NA JI BA TA YI MIN BA!
Wani mai sana’anta akwatin gawa ne aka kawo masa aikin yin akwatin ana bukatarsa da gaggawa, bayan ya gama ya sa a motarsa zai kai, yana cikin tafiya sai ta lalace. Sai ya yi shawarar dauka a kai ya karasa. Yana cikin tafiya sai ’yan sanda suka tare shi suka tambaya, “Ina zuwa?” Sai ya ce “Wallahi makabartar da aka kai ni ce, na ji ba ta yi min ba, ina son in samu inda ba taro da yawa.” Sai ’yan sandan suka ruga a guje suka bar shi.
0 Reviews