Read more
![]() | |
www.alhaqqblog.com.ng |
Wani dan asalin kasar indiya me suna Chiuhatma Basu a lokacin wani biki a Bangalore ta kasar india ya aure macen bera.
Basu dai ya rasa matarsa ne a sanadiyyar hatsarin mota a watan Janairun Bana Ya aure macen beran ne saboda, kamar yanda ya ruwaito "Auren ze sama wa Matattar matar tasa salama a rayuwarta ta gaba"
Kamfanin dillacin labarai ta worldnews tace," Mutumin dan kimanin shekaru 41 sannan me yara 4 ya samu zautuwar hankali har na tsawon wata daya. Se kwatsam suka yi ido hudu da wannan Kyakkyawar santaleliyar macen berar.
Basu Yace, " Wannan budurwar beran wata ran ta bayyana a kofar dakina tare da hancintata da idanunta sak na matana."
Mr Chuhatma Basu Ya ci gaba da cewa, "A cikin wannan yanayin ne kawai se ya fahimce akwai alaka tsakanin kwanciyar salamar matarsa da kuma auren wannan berar. Daga nan ne se ya afka kicin domin girka mata nau'in abincin da matarsa tafi so."
A cewarsa " wannan yar kusun nada matukar daukar hankali sannan yanda matarsa keda kallon daukar hakali haka itama berar take.
Wani malamin addinin Hindu ya shaidawa Basu cwa lallai ya kasance me matukar sa'a, sannan auren beran da yayi ze sama wa matar tasa salama.
Wannan aure mara kan gado dai duk da rashin tsarinsa, an yarda da shi a dokar kasar Indiya sannan ba shi bane na farko.
Tabdi jam wata miyar se a makobta.
0 Reviews